Shugaban tawagar gwamnatin Syria Bashar al-Ja'afari, ya ce kungiyar Jabhat al-Nusra, ta taba kame ikon yankin ruwa dake samarwa al'ummar birnin Damascus ruwan sha, kuma ta sa jama'ar birnin kasa samun ruwan sha har tsawon kwanaki 42. Duk da haka tsagin 'yan adawar basu dauke su a matsayin 'yan ta'adda ba.
Kaza lika Al-Ja'afari ya soki 'yan adawar da murde ma'anar yarjejeniyar tsagaita wuta.
Sai dai a nasa bangare, jagoran wakilan 'yan adawar Mohammed Alloush, cewa yayi halartar wakilan masu tada kayar baya a Syria da kasar Iran ke daukar nauyi bai dace ba, kuma zai sanya a fuskanci matsaloli wajen cimma kudurin tsagaita bude wata.
An dai bude taron shawarwari na birnin Astana ne a jiya Litinin, kuma sassan gwamnatin Syria da 'yan adawa, tare da sauran masu ruwa da tsaki na Rasha da Turkiyya da MDD sun halarci taron.
Kaza lika an gayyaci jakadan Amurka dake Kazakhstan George Krol, domin ya kasance cikin masu sanya ido ga gudanar taron.(Saminu Alhassan)