Wang ya bada shawarar cewa, na farko, a maida shirin neman ci gaba mai dorewa nan da shekarar 2030 a cikin manyan tsare-tsaren neman ci gaba na kasashen G20, na biyu, a ci gaba da ba da muhimmanci ga batun neman bunkasuwa cikin abubuwan da kasashen G20 za su tattauna a kai, da kuma sanya wannan batu cikin manufofin raya tattalin arziki na kasashen G20. Na uku shi ne, ya kamata kasashen G20 su dauki nauyi kafada da kafada domin neman ci gaba mai dorewa, ta hanyar la'akari da karfin kowace kasa. Wang ya kuma kara da cewa, ya zama dole bangarori daban-daban su ci gaba da nuna kwazo wajen aiwatar da yarjejeniyar Paris da aka daddale dangane da shawo kan matsalar sauyin yanayi.(Murtala Zhang)