in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wang Yi: Tsayawa kan manufar kasar Sin daya tak a duniya ya dace da halin da ake ciki
2017-01-12 14:07:21 cri
Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya gana da takwaransa na tarayyar Najeriya Geoffrey Onyeama a jiya Laraba a birnin Abuja. Bayan ganawar jami'an biyu, an shirya wani taron manema labarai, inda Mista Wang Yi ya ce, kasar Sin ta yabawa tarayyar Najeriya saboda tsayawar da ta yi kan manufar kasar Sin daya tak a duniya, da daukar matakai domin warware wasu matsaloli na tarihi.

Mr. Wang ya ce, tsayawa tsayin daka kan manufar kasar Sin daya tak a duniya, na dacewa da muradun jama'a, gami da hakikanin halin da ake ciki a yanzu.

Wang ya ce, a madadin gwamnatocin kasashen biyu, shi da Onyeama sun rattaba hannu kan wata sanarwar hadin-gwiwa, inda Najeriya ta amince cewa, Taiwan wani yanki ne da ba za a iya balle shi daga kasar Sin ba, kuma ta yi alkawarin cewa, ba za ta yi duk wata mu'amala ta fuskar gwamnati tare da Taiwan ba.

A daya bangaren kuma, Najeriya ta jaddada goyon-bayanta ga kokarin da gwamnatin kasar Sin take yi, na tabbatar da cikakken yankin kasa. (Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China