in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Abbas: Palasdinu ba za ta yi watsi da shirin kafa kasashe 2 ba
2017-02-16 20:59:21 cri

A Alhamis din nan ne kamfanin dillancin labaru na al'ummar Palasdinu, ya kaddamar da sanarwar shugaba, wadda ke cewa shugaba Mahmoud Abbas, da al'ummarsa ba za su taba watsi da "shirin kafa kasashe 2" ba, za kuma su kawo karshen mamayar da Isra'ila take yi a yakunan su cikin gaggawa bisa dokokin duniya.

Kaza lika shugaba Abbas, ya ce za a kai ga kafa kasar Palasdinu bisa iyakar da aka shata a shekarar 1967, inda kuma za a mayar da gabashin Kudus a matsayin hedkwatar kasar.

Abbas ya fadi hakan ne a matsayin martani kan kalamin shugaban Amurka Donald Trump, a yayin taron manema labaru da shugaban na Amurka ya gudanar a jiya tare da firayin ministan kasar Benjamin Netanyahu, wanda ke ziyara a Amurka. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China