in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Isra'ila ta yi watsi da kudurin MDD game da matsugunan Yahudawa
2016-12-24 13:30:55 cri
Kasar Isra'ila ta sanar a daren jiya Juma'a cewa, ta yi fatali da kudurin dokar kwamitin tsaro na MDD wanda ya bukaci a kawo karshen takaddama game da matsugunan yahudawa, tace sam ba zata mutunta kudurin dokar ba.

Sanarwar da ofishin firaministan Isra'ilan Benjamin Netanyahu ya fitar, ta yi Allah wadai da kudurin dokar kwamitin MDD, wanda ya bukaci a daina gina matsugunan nan da nan.

Kasashen Malaysia, New Zealand, Senegal, da Venezuela ne suka gabatar da kudurin, kuma mambobi kashe 14 ne suka kada kuri'ar amincewa da shi, yayin da Amurka ce kadai ta janye jiki daga jefa kuri'ar.

Ofisin Netanyahu, ya zargi shugaba Barack Obama da laifin iza wuta game da kudurin a asirce, zargin da fadar white house ta sha musantawa.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China