in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bana, shekara ta karshe wajen aiwatar da shirin kafa kasashen Palasdinu da Isra'ila, in ji Abbas
2017-01-19 11:12:01 cri

Shugaban Palasdinu Mahmoud Abbas ya ce, shekarar bana, ita ce shekarar karshe game da shirin kafa kasashen Palasdinu da Isra'ila.

Shugaba Abbas ya bayyana hakan ne a jiya yayin shawarwari da takwaransa na kasar Poland Andrzej Duda da ke ziyara a birnin Bethlehem da ke yammacin gabar kogin Jordan. A yayin taron manema labaru bayan shawarwarin, mista Abbas ya ce, a yayin shawarwarin, ya gaya wa mista Duda sakamakon da aka samu a yayin taron zaman lafiya na Gabas ta Tsakiya da aka gudanar a Paris da kuma kokarin da kasashen duniya suke yi wajen aiwatar da shirin na kafa kasashen Palasdinu da Isra'ila. Ya kuma nuna cewa, Palasdinawa sun dade suna daddale yarjejeniyar zaman lafiya kan wannan batu.

Har ila yau, mista Abbas ya zargi yadda Donald Trump, shugaban kasar Amurka mai jiran gado yadda yake yunkurin canja matsugunin ofishin jadakancin Amurka da ke Isra'ila daga Tel Aviv zuwa birnin Kudus, matakin da tabbas din ya ce zai kawo cikas ga shirin shimfida zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China