in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilin kasar Sin ya yi kira ga Palasdinu da Isra'ila da su koma teburin  shawarwari
2016-12-24 13:43:33 cri
Mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD, Wu Haitao a jiya Asabar ya bayyana cewa, kasar Sin na maraba da yadda kwamitin sulhu na MDD ya zartas da kudurin da ya shafi batun matsugunan Isra'ila a wannan rana, kuma tana ba wa bangarorin biyu kwarin gwiwar sauke nauyin da ke wuyansu, kuma su tabbatar da natsuwa da hakuri tare da kulla aminci da juna, ta yadda za su koma kan teburin shawarwari tun da wuri.

Kwamitin sulhu na MDD a wannan rana ya zartas da kuduri mai lambar 2334, inda ya jaddada cewa, yadda Isra'ila ke gina matsugunanta a filayen Palasdinawa da ta mamaye ya saba da dokokin kasa da kasa, don haka, an kalubalanci Isra'ilan da ta daina wannan aiki.

A jawabin da ya gabatar bayan jefa kuri'ar, Mr. Wu Haitao ya bayyana cewa, kasar Sin na nuna goyon baya ga kwamitin sulhun da ya taka rawar da ta kamata a kan batun Palasdinu, kuma yadda kwamitin ya zartas da kudurin na da muhimmiyar ma'ana, abin da ya bayyana burin bai daya na gamayyar kasa da kasa, wanda kuma ya amsa kiran kasashen Palasdinu da Larabawa.

A wannan rana, babban sakataren MDD Ban Ki-moon ta bakin kakakinsa ya bada sanarwa, inda ya yi maraba da wannan kudurin da kwamitin sulhu na MDD ya zartas.(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China