in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kawancen kasashen Larabawa ya yi maraba da kudurin MDD game da matsugunan Yahudawa
2016-12-25 13:12:50 cri
Kawancen kasashen Larabawa a jiya Asabar ya fitar da sanarwa, inda ya yi maraba da kudurin da kwamitin sulhun MDD ya fitar a ranar Jumma'a wanda ya shafi batun matsugunan Yahudawa. A wannan rana da dare kuma, firaministan kasar Isra'ila Benjamin Netanyahu ya bayyana cewa, kasar ta Isra'ila za ta sake tantance huldarta da MDD.

A sanarwar da kawancen kasashen Larabawa ya fitar, kawancen ya nuna maraba da kudurin na kwamitin sulhun MDD, inda babban sakataren kawancen Ahmed Abul-Gheit ya bayyana cewa, kudurin ya samu goyon bayan daukacin mambobin kwamitin, kuma ya kasance mai muhimmanci da kwamitin ya zartas a cikin 'yan shekarun baya game da batun Palasdinu da Isra'ila. Don haka, ya taya gwamnatin Palasdinu da al'ummarta murna. Mr.Abul Gheit ya ce, yadda aka zartas da wannan kuduri ya shaida goyon bayan gamayyar kasa da kasa kan gwagwarmayyar gwamnatin Palasdinu da jama'arta ta neman kafa kasar Palasdinu mai 'yancin kanta da ke da babban birninta a gabashin Jeruselem. Ya kuma yi fatan zartas da wannan kuduri zai matsa wa Isra'ila lamba, ta yadda kasar za ta bi jerin yarjejeniyoyin kasa da kasa da suka hada da wannan kuduri.

Sai kuma a wani bikin gargajiya na Yahudawa da aka shirya a ranar 24 ga wata da dare, Mr. Netanyahu ya gabatar da jawabi, inda ya yi suka ga wannan kuduri na kwamitin sulhu, kuma ya ce Isra'ila ko kadan ba za ta amince da shi ba. Ya kara da cewa, Isra'ila za ta sake kimanta huldarta da sassan MDD cikin wata guda, ya kuma ba da umurnin rage biyan kudin ga wasu sassa 5 na MDD. (Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China