Jiya Talata 14 ga wata, ma'aikatar al'adu da kimiyya ta kasar Japan, ta ba da jagoranci na ilmantarwa ga 'yan makarantar firamare da na midil, inda a karo na farko, ta bukaci a ilmantar da kananan yaran kasar cewa, wai tsibirin Diaoyu yanki ne na Japan.
Dangane da lamarin, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya bayyana a yau Laraba cewa, kasar Sin na kalubalantar Japan game da girmama tarihi, ta daina tsokana, ta hanyar yada wa kananan yara ra'ayoyi marasa tushe, ta kuma yi kokarin daukar hakikanin matakai, na kyautata huldar da ke tsakanin ta da Sin. (Tasallah Yuan)