in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta yi watsi da hadin gwiwar Japan da Amurka game da batun yankin kasa
2017-02-13 19:51:24 cri

Kwanan baya, kasashen Japan da Amurka sun ba da wata sanarwar hadin gwiwa, inda suka yi shelar cewa, "yarjejeniyar tsaro tsakanin Amurka da Japan" tana shafar tsibirin Diaoyu.

Dangane da wannan lamari, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya jaddada yau Litinin a yayin taron manema labaru da aka saba shiryawa a nan Beijing cewar tsibirin Diaoyu da tsibiran da ke makwabtaka da shi, yankin kasar Sin ne tun fil azal. Kuma kamata ya yi Japan da Amurka su yi taka tsan-tsan, kan kalamansu da aikace-aikacensu, su daina kalaman da ba su dace ba.

Kaza lika bai dace su yamutse gaskiyar batun ba da abubuwan da suka shafe shi. Ya ce hakan zai kawo illa ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a shiyyar da Sin da Japan suke ciki. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China