in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta bukaci kasar Japan da ta yi kokarin kyautata huldar dake tsakanin kasashen 2
2017-02-07 19:32:38 cri
Mista Lu Kang, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, ya furta a yau Talata cewa, kasar Sin ta kalubalanci kasar Japan da ta canja ra'ayinta game da kasar Sin, sa'an nan ta yi ayyukan da za su taimakawa kokarin kyautata huldar dake tsakanin kasashen 2.

Kalaman kakakin gwamnatin kasar Sin na zuwa ne bayan wani labarin da kafofin watsa labaru na kasar Birtaniya suka bayar, cewa tun a shekarun baya, ofishin jakadancin kasar Japan dake Birtaniya yake biyan wata kungiyar Henry Jackson mai ba da shawarwari kan harkokin siyasa Fam dubu 10 a duk wata, ta yadda kungiyar za ta taimakawa kasar Japan yayata ra'ayin "barazanar kasar Sin a duniya" a kasar Birtaniya. Wannan shiri na Japan ya shafi wasu tsoffin manyan jami'an gwamnatin kasar Birtaniya, gami da manyan hafsoshin kasar da suka riga suka yi ritaya.

Dangane da batun, Mista Lu Kang ya bayyana cewa, idan har wannan labarin ya tabbata, to, hakaki ba zai haifar da da mai ido ba. A cewarsa, kasar Japan ta kan yi kira da a daidaita huldar dake tsakaninta da kasar Sin, amma a hannu guda kasar tana kokarin shafawa kasar Sin kashin kaji, hakan ya nuna rashin gaskiyar kasar Japan a fili.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China