in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Otel din APA na Japan zai janye littattafan da suka karyata kisan kiyashin da maharan Japan suka aikata a Nanjing
2017-01-26 20:33:36 cri

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ta shaida wa taron manema labaru yau Alhamis cewa, kwanan baya, babban sakataren kwamitin shirya gasar wasannin motsa jiki na lokacin hunturu ta Sapporo ya aika wa kwamitin wasannin Olympic na kasar Sin wata wasika a hukumance, inda ya ce, otel din APA ya tsai da kudurin janye dukkan littattafan da aka wallafa bayanai kisan Sinawan da mahara na Japan suka aikata daga dakunan kwana, babban zaure da sashen kula da baki na otel din. Kasar Sin tana fatan Japan za ta cika alkawarinta, a kokarin tabbatar da gudanar da gasar yadda ya kamata.

Otel din APA na Japan ya dade yana gwada littattafan da suka musunta kisan kiyashin da maharan Japan suka aikata a birnin Nanjing na kasar Sin a shekarar 1937 da kuma batun matan da sojojin Japan din suka yi lalata da su. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China