in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ba za ta yarda a bata ran jama'ar kasarta ba
2017-01-24 19:44:54 cri

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin madam Hua Chunying ta shaida wa taron manema labarai a yau Talata cewa, kisan-kiyashin da maharan kasar Japan suka yi a birnin Nanjing na kasar Sin a shekarar 1937, inda suka kashe Sinawa kimanin dubu 300, yana nan a cikin tarihi, kuma kasashen duniya na ganin cewa, babu abin da zai kankare wannan tabar-gaza. Kasar Sin ba za ta yarda a yi karin gishiri a bayanan tarihi, ko kuma a ci mutuncin al'ummarta ba.

Kwanan baya, magajin garin birnin Nagoya na kasar Japan Kawamura Takashi ya musanta kisan-kiyashin da maharan Japan din suka aikata a birnin Nanjing. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China