in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan harkokin wajen Sin zai gana da takwaransa na kasar Japan
2016-08-23 19:52:22 cri

Rahotanni na nuna cewa, da alamun ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi zai gana da takwaransa na kasar Japan Fumio Kishida, yayin da jami'an za su halarci taron ministocin harkokin wajen kasashen Sin, Japan da Koriya ta Kudu karo na 8 da zai gudana ranar Laraba a birnin Tokyo na kasar Japan.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang wanda ya bayyana hakan yau Talata a nan birnin Beijing, ya ce Wang zai halarci taron ne bisa gayyatar da aka yi masa.

Lu Kang ya ce, kamar yadda aka saba, yayin ganawar sassan uku za su yi musayar ra'ayoyi, duk da adawar da kasashe makwabta da al'ummomin kasa da kasa suke nunawa game da matakan da Japan ta ke dauka dangane da batun tekun kudancin kasar Sin.

Ana sa ran Wang Yi zai bayyana matsayin kasar Sin game da wannan batu, kana ya bukaci Japan za ta yi kokarin dawo da huldar da ke tsakanin kasashe biyu kan turbar da ta dace.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China