in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kakakin ma'aikatar tsaron kasar Sin ya yi jawabi game da takardar bayani game da tsaro ta shekarar 2016 da kasar Japan ta gabatar
2016-08-03 10:43:30 cri
A jiya Talata ne, kakakin ma'aikatar tsaron kasar Sin Wu Qian ya yi jawabi game da farar takarda game da harkokin tsaro ta shekarar 2016 da kasar Japan ta gabatar, inda ya bayyana cewa, farar takardar da ma'aikatar harkokin tsaro ta kasar Japan ta gabatar ba ta canja abubuwa da ta ke fada ba game da aikin tabbatar da tsaro da yadda kasar Sin ta ke raya harkokin ta na soja, da bayanai game da batun tekun kudancin kasar Sin da na gabashin kasar Sin, inda aka yi bayanan da ba su dace ba game da sojojin kasar Sin, da tsokana kan dangantakar dake tsakanin Sin da kasashen dake dab da ita, kana ta yaudari kasashen duniya.

Rundunar sojojin kasar Sin ba ta ji dadin abubuwan da Japan din ta rubuta ba, wannan ya sa ta tuntubi kasar Japan game da wannan batu.

Wu Qian ya bayyana cewa, burin Japan na wallafa wannan takarda shi ne neman dalilin da zai ba ta damar kyautata manufofinta na aikin soja da kara kera makamai da na'urorin aikin soja, har ma ta gyara kundin tsarin mulkinta game da batun tabbatar da zaman lafiya, a saboda haka, kamata ya yi kasashen duniya su kara yin hattara da kasar ta Japan. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China