A shekarar 2013 ne, Tsohon Shugaban kasar Gambia Yahaya Jammeh, ya janye kasar daga kungiyar, yana mai zarginta da ci da gumin kasashe masu tasowa.
Yayin wani taron manema labarai jiya a Banjul, babban birnin kasar Gambia, Boris Johnson ya ce ya gana da shugaba Barrow, yana mai cewa, sabon Shugaban na kyawawan manufofin ciyar da kasar gaba.
Ya ce, yana alfaharin sanar da cewa, Gambia za ta koma kungiyar Commonwealth, inda ya ce ya tattauna da sakatare Janar ta Kungiyar, kuma ta kuduri niyyar gaggauta tabbatar da batun.
A jiya talata ne, sakataren harkokin wajen Birtaniyan ya isa Banjul, a wani bangare na ziyarar kwanaki biyu da ya kai Afrika. Zai kuma isa kasar Ghana, inda aka shirya zai gana da sabon shugaba kasar Nana Akufo- Addo. ( Fa'iza Mustapha)