Shugaban majalisar Dattijan kasar Bukola Saraki ne ya bayyana haka ga manema labarai a babban birnin kasar Abuja, jim kadan bayan wata ganawar sirri da suka yi da Mukaddashin Shugaban kasar Yemi Osinbajo.
Shugaban na majalisar dattiijai da ya samu rakiyar takwaransa na majalisar wakilai Yakubu Dogara, ya ce mukaddashin shugaban kasar ya yi musu karin haske game da ayyukan dakarun Nijeriya a kasar Gambia.
Nijeriya ta tura sojoji dari biyu da jirgin yaki zuwa Senegal, a wani bangare na kokarin tabbatar da sakamakon zaben kasar Gambia.
Sojojin dai, na cikin dakarun hadin gwiwa na kungiyar ECOWAS, da shugabanni kungiyar suka dorawa nauyin shiga tsakani, tare da tabbatar da aiwatar da sakamakon zaben shugaban kasar Gambia da aka yi ranar 1 ga watan Decemban 2016.(Fa'iza Mustapha)