A zantawarsa da 'yan jaridu, Mista Stephane Dujarric ya bayyana cewa, wakilin musamman na sakatare-janar na MDD mai kula da yammacin Afirka da Sahel, Mohamed Ibn Chambas, ya isa birnin Banjul a ranar Alhamis, inda zai ci gaba da tattaunawa tare da Adama Barrow kan halin da ake ciki a kasar ta Gambiya.
Stephane Dujarric ya kuma ce, Chambas zai yi shawarwari tare da shugaban majalisar dokoki, da wasu tawagogin jami'an diflomasiyya, gami da kungiyoyin fararen-hula na Gambiya, don ya tantance ofishin MDD mai kula da batutuwan yammacin Afirka da Sahel kan yadda zai taka rawa wajen taimakawa Gambiya mika mulki cikin lumana.(Murtala Zhang)