in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta alkawarta tallafawa mika mulki a kasar Gambia
2017-01-26 10:45:29 cri
Kakakin MDD Stephane Dujarric, ya ce wakilin musamman na MDDr mai lura da al'amura a yankunan yammacin Afirka, da yankin Sahel Mohamed Ibn Chambas, ya shaidawa kwamitin tsaron MDDr cewa, ofishin sa na UNOWAS, na daukar matakan da suka wajaba na tabbatar da mika mulki cikin nasara ga sabuwar gwamnatin kasar Gambia.

Dujarric, ya ce yayin zantawa da mambobin kwamitin na tsaro kai tsaye ta kafar bidiyo, Ibn Chambas, ya bayyana musu cewa ofishin sa na fatan ci gaba da goyon mayan matakan samun daidaito, da yafiya, tare da dinkewar sassan al'ummar Gambia.

Ya ce tuni tawagar UNOWAS ta girke dakarun ta a kasar, domin tabbatar da nasarar mika mulki ga zababben shugaban kasar Adama Barrow, wanda ake fatan zai koma Gambia nan gaba a yau Alhamis.

Ana sa ran Mr. Barrow zai bar birnin Dakar na kasar Senegal, zuwa gida Gambia bisa rakiyar Mr. Chambas. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China