in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin Amurka da Isra'ila sun tattauna kan dangantakar dake tsakanin kasashen da kuma tsaro
2017-01-23 10:26:55 cri
Shugaban Amurka Donald Trump da Firayiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, sun gana a jiya ta wayar tarho, inda suka tattauna game da yadda za su karfafa dangantakar dake tsakaninsu, da tsaro da kuma samar da kwanciyar hankali a yankin gabas ta tsakiya.

Wata sanarwa da fadar White House ta fitar, ta ce Trump ya jadadda muhimmancin da Amurka ta ba dangantakar dake tsakaninta da Isra'ila, ta fuskar ayyukan soji da bayanan sirri da kuma tsaro, yana mai cewa alama ce dake nuna zurfin danganka tsakanin kasashen biyu.

Shugabannin, sun amince da ci gaba da tattauna batutuwa da suka shafi yankunansu, ciki har da magance barazanar daga Iran.

Sanarwar ta ruwaito Trump na jaddada kudurinsa na taimakawa wajen tabbatar da tsaro a Isra'ila, yana mai jaddada aniyar gwamnatinsa ta yaki da kungiyar IS da sauran kungiyoyi masu tsattsauran ra'ayi.

Har ila yau, Trump ya jaddada cewa, samun zaman lafiya tsakanin Isra'ila da Falasdinu, abu ne da ya dogara kan cimma yarjejeniya kai tsaye tsakaninsu, inda ya ce Amurka za ta hada hannu da Isra'ila domin cimma wannan manufa.

Yayin ganawar, Shugaba Donald Trump ya kuma gayyaci Netanyahu domin su tattauna a fadar White House cikin kwanakin farko-farko na watan Fabreru. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China