A cikin sanarwar karshe da aka fitar, mahalarta taron, sun jaddada muhimmancin cigaba da daukar matakan tattaunawa a matsayin hanyar magance takaddamar dake tsakanin kasashen na Israel da Palastinu, ta yadda za'a samu zaman lafiya da tsaro cikin dogon lokaci a tsakaninsu.
Bayan wani taro na wuni guda a babban birnin kasar Faransa, wanda wakilan kasashe sama da 70 suka halarta da kungiyoyin alumma, sun jaddada muhimmancin bangarorin da abin ya shafa su zauna a teburin sulhu don warware rikicin, kuma a dauki karin matakai da za su kawo karshen tashin hankalin. Kana a hanzarta fara tattaunawar sulhun mai amfani ba tare da bata lokaci ba.
Sun kuma bayyana cewa bai dace wani bangare ya yi gaban kansa ba, wanda hakan lamari ne da zai iya gurgunta duk wani yunkuri na warware takaddamar, wannan ya hada da batun Jerusalem, da kan iyakoki, da tsaro da kuma batun 'yan gudun hijira. (Ahmad)