in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sakataren harkokin kasashen waje na Burtaniya yana ziyara a kasar Sin
2015-08-14 09:24:12 cri
A jiya ne sakataren harkokin kasashen waje na Burtaniya Philip Hammond ya iso birnin Beijing gabanin ziyarar aikin da shugaba Xi Jinping na kasar Sin zai kai kasar ta Burtaniya a watan Oktoba.

A jawabinsa yayin da ya ke jagorantar wata tattaunawar manyan tsare-tsare da Hammond, Mamba a majalisar gudanarwar kasar Sin Yang Jiechi ya ce, ziyarar da shugaba Xi zai kai kasar ta Burtnaiya za ta kara bunkasa hadin gwiwar kasashen biyu. Kuma kasar Sin a shirye ta ke ta yi aiki da Burtaniya wajen daga matsayin dangantakar kasashen biyu zuwa wani sabon matsayi.

Mr Yang ya ce, kasar Sin tana fatan yin aiki tare da al'ummomin kasa da kasa ciki har da kasar Burtaniya, domin kiyaye irin nasarorin da aka samu bayan yakin duniya na biyu da kuma ka'idojin MDD.

A nasa jawabin Mr Hammond ya bayyana kudurin kasarsa na cin gajiyar hadin gwiwar da ke tsakanin kasashen biyu, musamman ma karkashin tsarin nan na ziri daya da hanya daya. Kasar ta Burtaniya dai ita ce kasa ta farko a nahiyar turai da ta shiga cikin bankin samar da kayayyakin more rayuwa na Asiya wato AIIB.

Alamu na nuna cewa, kasashen Sin da Burtaniya na iya daga matsayin hadin gwiwar da ke tsakaninsu tare da sanya hannu kan wasu manyan yarjejeniyoyi a lokacin ziyarar ta shugaba Xi.

A watan Oktoban wannan shekara ce ake sa ran shugaba Xi Jinping na kasar Sin zai kai ziyara kasar Burtaniya bisa gayyatar sarauniya Elizabeth ta biyu.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China