A wasan karshe na rukuni na D na gasar cin kofin kwallon kafan Afirka wato AFCON da ya gudana a jiya Laraba, kasar Masar ta doke kasar Ghana, wadda ta riga ta samu nasarar fita daga rukunin na D, yanzu kasashen biyu su biyu sun samu nasara kaiwa zagaye na gaba na gasar
A ranar Asabar ne za a fara buga zagaye na gaba na gasar, inda kasar Burkina Faso za ta kara da kasar Tunisiya, yayin da kasar Senegal za ta kece reni da kasar Kamarun, sai kuma Masar wadda za ta fafata da kasar Morocco, Ghana kuma za kara da kasar Congo (Kinshasa). (Tasallah Yuan)