Bayan an fitar da kasar Tunisia da masanan wasannin motsa jiki na kasar Tunisia da na kasashen waje musammun ma na kasar Faransa da suka kimanta da rashin adalaci a gasar cin kofin Afrika ta shekarar 2015, shugaban kungiyar kwallon kafa ta Tunisia (FTF) Wadi Jary ya yi marubus daga kwamitin shirya wasannin na Afrika dake mamba tun cikin watan Mayun shekarar 2013, in ji kungiyar FTF a ranar Lahadi.
Haka kuma shi ma, tsohon mamban FTF, Chiheb Belkhria ya yi murabus daga mukaminsa a cikin kwamitin harkokin kudi na kungiyar CAF domin yin allawadai da yadda alkalin wasa ya jagoranci wasar da hada Tunisia da Guinea Ecuatorial.
A ranar Asabar da yamma, kungiyar 'yan wasan Tunisia da ake kira da "Aigles de Carthage" sun rasa tikitinsu na wasan daf da na kusa da karshe a cikin wasan da ta hada da su da 'yan wasan kasar Guinea Ecuatorial, da ci 2 da 1, bayan an kara lokacin wasa. Kungiyar Tunisia ta kasance ta farkon rukuninta, bayan ta taka leda a farkon zabin wasa, 'yan wasan Tunisia na cin wasa 1 da 0 har karshen mintoci 90, kafin a ga alkalin wasa dan kasar Mauritius, Rajindraparsad Seechurn ya busa bugun daga kai sai mai tsaron raga da yawancin masu shirya wasan suke ganin ba ya da dalili, a cewar masu fashin bakin wasan kwallon kafa, bisa la'akari da bayanan dan jaridar dake rawaito labarin wasan da ta hada Tunisia da Guinea Ecuatorial.
Tun bayan busa wasan karshe na wasan daf da na kusa da karshe tsakanin Tunisia da Guinea Ecuatorial, alkalin wasan kasar Mauritius ya sha suka daga kafofin watsa labarai na kasar Tunisia har da wasu 'yan jaridar wasannin motsa jiki daga kasashen waje dake kimanta alkalancin wasan da abin magudi. (Maman Ada)