Kasar Ghana ta kai ga wasan karshe a gasar cin kofin kwallon kafar Afirka na bana, bayan da ta doke mai masaukin baki Equatorial Guinea da ci 3 da nema, yayin wasan da suka buga jiya Alhamis.
Wannan wasa dai ya gamu da cikas, sakamakon hatsaniya da magoya bayan Equatorial Guinea suka tayar lokacin da Ghana ta jefa kwallo ta 3 a raga, lamarin da ya sanya alkalin wasan dakatar da wasan har tsahon mintuna 40.
Jami'an tsaro sun yi amfani da kulake da hayaki mai sa hawaye, domin kare 'yan wasan daga fushin 'yan kallon na Equatorial Guinea.
Yanzu haka dai Ghana za ta fafata ne da kasar Cote d'Ivoire, a wasan karshe da za a yi a filin wasa na Bata a ranar Lahadi. A shekarar 1992 ma dai kasashen biyu sun hadu a wasan karshe na gasar ta AFCON, kuma sai da ta kai su ga bugun daka kai sai mai tsaron gida, kafin Cote d'Ivoire ta samu nasarar lashe kofin na wancan karo.
A gobe Asabar ne kuma za a buga wasan neman matsayi na uku, tsakanin janhuriyar dimokadiyyar Congo da Equatorial Guinea. (Saminu)