in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AFCON: An ci tarar Equatorial Guinea sakamakon tada hargitsi a filin wasa
2015-02-07 20:26:31 cri
Hukumar CAF ta ci tarar Equatorial Guinea dalar Amurka 100,000, sakamakon yamutsi da 'yan kallon kasar suka tayar, yayin wasan daf da na karshe da kasar ta buga da Ghana a ranar Alhamis.

Rahotanni sun tabbatar da jikkatar mutane 36, an kuma garzaya da 14 daga cikin su zuwa asibiti. An ce magoya bayan Equatorial Guinean sun rika jifa da kwalabe, da duwatsu domin nuna fushin rashin nasarar da suka samu, bayan da Ghana ta jefa kwallon ta ta 3 a zare.

Halin rudanin da aka shiga ya yin wasan na ranar Alhamis, sai da ya kai ga dakatar da taka leda har kusan rabin sa'a, lokacin da magoya bayan Ghana ke kokarin tserewa fushin 'yan Equatorial Guinea.

A wani ci gaban kuma hukumar CAF ta ci tarar kasar Morocco kudi sama da Euro miliyan 8, bisa kin amincewa da kasar ta yi, ta karbi bakuncin gasar ta nahiyar Afirka ta bana.

Hukumar ta CAF ta kuma dakatar da kasar daga halartar gasannin nahiyar da za a buga a shekarun 2017 da ta 2019, kari kan dakatarwar da aka yiwa kasar daga halartar gasar bana.

Tun da fari dai Morocco ta bukaci CAF ta dage lokacin gudanar gasar dake daf da kammala a yanzu haka, bisa tsoron kada a samu bullar cutar Ebola cikin kasar sakamakon gudanar gasar. Daga bisani ne kuma aka baiwa Equatorial Guinea damar karbar bakuncin gasar.

A yau ne kuma Equatorial Guinea za ta buga wasan neman matsayi na uku ita da jamhuriyar dimokaradiyyar Congo. Yayin da a gobe Lahadi kuma Ghana za ta fafata da Ivory Coast, a wasan karshe na gasar ta bana.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China