Kasar Cote d'Ivoire ta lashe gasar cin kofin Afrika AFCON karo na 30 da aka gudanar a kasar Guinea Equatorial bayan ta doke kasar Ghana da ci 9 da 8 a yayin bugun daga kai sai mai tsaron gida, bayan sun murza leda a tsawon minitoci 90 na wasa ba tare da zura kwallaye ba a ranar Lahadi a Bata.
Wannan ne karo na biyu da kasar Cote d'Ivoire take daukar kofin Afrika bayan ta dauka a shekarar 1992. Yau da kusan shekaru 23 da suka wuce, kasar Cote d'Ivoire ta taba fafatawa tare da kasar Ghana a gasar karshe. (Maman Ada)