in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ma'aikatan Trump a fadar White House sun yi rantsuwar kama aiki
2017-01-23 20:31:07 cri

A jiya Lahadi ne, shugaba Donald Trump na kasar Amurka da mataimakinsa Mike Pence suka jagoranci wani biki a zauren dake gabashin fadar White House, inda manyan jami'a fiye da 20 da za su aiki a matsayin ma'aikatan fadar ta White House suka yi rantsuwar kama aiki. Su dai wadannan ma'aikata babu bukatar mika sunayensu ga majalisar dattawan kasar don samun amincewarsu.

Jaridar The Washington Post ta Amurka ta ruwaito Trump yana fada a yayin bikin cewa, zai maido da shawarwari game da yarjejeniyar yin ciniki ba tare da shinge ba ta arewacin nahiyar Amurka da kuma batun tsaro a bakin iyakar kasashen Amurka da Mexico. Ya kuma yi hasashen cewa zai shafe shekaru 8 yana mulkin kasar ta Amurka. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China