in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta yi watsi da tura tawaga da Taiwan ta yi bikin rantsar da Trump
2017-01-20 19:43:20 cri
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying, ta ce Sin ta yi watsi da matakin yankin Taiwan, na tura tawagar kashin kai, domin halartar bikin rantsar da sabon shugaban kasar Amurka Donald Trump.

Uwar gida Hua ta ce hakan, wani mataki ne da ya sabawa akidar da kasashen Sin da Amurka suka amincewa, kuma Taiwan din na yin hakan ne, domin gurgunta kyakkyawar alakar dake tsakanin Sin da Amurka.

Da take jawabi yayin taron manema labarai da ya gudana a Juma'ar nan, Hua ta ce wasu daga kusoshin Taiwan ne suka kitsa wannan tsari na tura tawagar, duk kuwa da cewa Sin ta sha nanata rashin amincewar ta da aikata hakan.

A daya bangaren kuma, jami'ar ta bayyana cewa ita kan ta Amurka, ta tabbatar da cewa, za ta gayyaci ofisoshin kasashen ketare dake Amurkan ne kawai, maimakon aikawa kasashe da yankuna goron gayyatar bikin rantsuwar sabon shugaban.

Kalaman uwar gida Hua na zuwa ne, bayan da wasu kafafen watsa labaru suka fidda wasu rahotanni dake cewa, tsohon kusa a gwamnatin yankin na Taiwan Yu Shyi-Kun, ya jagoranci wata tawagar wakilai daga yankin, domin zuwa birnin Washington, inda za a yi bikin rantsuwar Mr. Trump.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China