in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi zanga-zanga da taya murna a lokaci guda, yayin da Trump ya yi rantsuwar kama aiki a matsayin Shugaban Amurka
2017-01-21 14:04:55 cri

A cikin yanayin taya murna tare da zanga-zanga, Donald Trump ya yi rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban Amurka na 45 a birnin Washington da tsakar ranar jiya, inda ya yi jawabin kama aiki mai taken "makomar Amurka a matsayin aikin da ya sha gaban komai'.

A wannan rana da safe, masu nuna goyon baya ga Trump da masu adawa da shi, sun taru a birnin Washington.

Kafin bikin rantsuwar kama aikin, masu zanga-zanga fiye da dari daya sun lalata motoci da tagogin kantuna a tsakiyar birnin.

Bayan kammala jawabin nasa, kuma kafin fara bikin taya murnar ne rikicin ya tsananta, al'amarin da ya kai 'yan sanda ga yin amfani da barkonon tsohuwa don tarwatsa masu zanga-zanga.

Rundunar 'yan sandan birnin Washington ta bayyana cewa, an riga an kama masu zanga-zanga 217.

An gabatar da matsayin gwamnatin Trump na mai da hankali kan fannonin makamashi da harkokin waje da kuma tattalin arziki a shafin intanet na fadar shugaban kasar wato White House.

An kuma sanar da cewa, za a soke shirin fuskantar sauyin yanayi da gwamnatin Barack Obama ta gabatar.

Kafin ranar rantsuwar kama aikin, kungiyar masu adawa da sabuwar gwamnatin ta yi zanga-zanga, inda yawansu ya fi na ranar rantsuwar dukkan tsofaffin shugabannin kasar.

A yau 21 ga wata ma, an yi zanga-zanga mai taken "zanga-zangar mata" a birnin Washington da wurare da dama dake kasar Amurka, kuma yawan wadanda suka shiga zanga-zangar a birnin Washington kadai ya kai dubu 200. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China