in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi zanga-zangar kin amincewa da Trump
2017-01-23 11:15:28 cri
Masu zanga zanga sun yi fitar dango kan tituna da dama a sassan kasar Amurka da ma kasashen duniya domin nuna adawa da sabon shugaban Amurka Donald Trump. Hakan na faruwa ne a yayin da Mr. Trump yayi rantsuwar kama aiki a matsayin sabon shugaban kasar Amurkan a ranar 20 ga watan nan.

Rahotanni na cewa, an yi zanga-zanga a birane fiye da 20 dake sassan duniya daban daban domin kin amincewa da Trump bisa ra'ayoyinsa dake shafar nuna bambancin launin fata, da bambanci tsakanin maza da mata, da bada kariya ga cinikayya da dai sauransu. An ce, mutane fiye da miliyan daya sun halarci zanga-zangar.

Sai kuma a kasar Amurka, mata sun yi zanga-zanga a biranen Washington, New York, Chicago, Los Angeles da sauransu, a ranar ta asabar, masu zanga-zangar da yawancinsu mata, sun yi taruka cikin lumana, suna masu bukatar Trump ya girmama ikon mata, da tabbatar da moriyar su, tare da fatan sabuwar gwamnatin kasar za ta nuna goyon baya ga ikon jama'a, da kin amincewa da nuna bambancin launin fata.

Ban da kasar Amurka, zanga-zangar kin amincewa da Trump ta yi kamari a birnin London na kasar Birtaniya. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China