in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Donald Trump ya yi rantsuwar kama aiki a matsayin sabon shugaban kasar Amurka
2017-01-21 14:04:06 cri

Zababben Shugaban kasar Amurka Donald Trump, ya yi rantsuwar kama aikin a matsayin shugaban kasar na 45 a birnin Washington, a jiya Juma'a 20 ga wata.

Babban alkalin kotun kasar, John G. Roberts ne ya jagoranci bikin rantsuwar.

Daga bisani, Trump ya yi jawabin kama aiki, inda ya jaddada alkawarin da ya yi yayin da yake yakin neman zabe, wato sanya makomar kasar Amurka a matsayin abun da ya fi komai muhimmaci.

Trump ya bayyana cewa, gwamnatin Amurka bisa jagorancinsa, za ta yi kokarin inganta rayuwar ma'aikata da daukacin al'ummar kasar ta hanyar gabatar da manufofi a fannonin da suka hada da cinikayya, haraji, kaura zuwa kasashen waje da harkokin kasashen waje da dai sauransu.

Sannan, ya jaddada cewa, tabbatar da sayan kayayyakin da aka sarrafa a Amurka da kara daukar ma'aikata 'yan kasar, su ne ka'idoji biyu mafi muhimmanci da zai maida hankali kansu yayin da yake kan karagar mulki.

Trump ya bayyana lashe zabe da ya yi na shugabancin kasar a matsayin nasara ga fararen hula, inda ya zargi bangaren siyasa na kasar da nuna halin ko-in-kula ga fararen hula tsawon lokaci.

Har ila yau, a jiyan ne, mataimakin shugaban kasar Mike Pence shi ma ya yi rantsuwar kama aikin. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China