in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatocin kasashe da dama suna sa ran hadin gwiwa da sabuwar gwamnatin Amurka
2017-01-22 13:30:50 cri
Zababben shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi rantsuwar kama aikin a matsayin shugaban kasar na 45 a birnin Washington a ranar Juma'a 20 ga wannan wata.

Bayan rantsuwarsa a wannan rana, shugabanni da jami'an gwamnatocin kasashe da dama sun nuna kyawawan fatansu na yin hadin gwiwa da sabuwar gwamnatin kasar Amurka dake karkashin jagorancin shugaba Trump, yayin da kuma cimma matsayi daya kan wasu batutuwan dake shafar hankulan kasa da kasa.

Haka kuma, cikin wata sanarwar da fadar shugaban kasar Masar ta fitar, an ce, shugaban kasar Abdel Fattah al-Sisi yana sa ran samun bunkasuwar dangantaka dake tsakanin kasarsa da kasar Amurka cikin shekaru hudu masu zuwa, watau lokacin da shugaba Trump yake kan ragamar mulkin kasar Amurka, domin bautawa al'ummomin kasashen biyu.

Kana, cikin sanarwar, an kuma bayyana cewa, ci gaba da hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu, da kuma yin shawarwari kan manyan batutuwan dake shafar shiyya-shiyya, zai taimaka wajen shimfida zaman lafiya da lumana a yankin Gabas ta Tsakiya, da samun bunkasuwa a yankin.

Haka zalika, fadar shugaban kasar Falesdinu ta fidda wata sanarwa cewa, shugaban kasar Mahmoud Abbas yana sa ran hadin gwiwar dake tsakanin gwamnatin kasarsa da gwamnatin kasar Amurka dake karkashin jagorancin shugaba Trump, ta yadda za a cimma burin shimfida zaman lafiya a yankin.

Bugu da kari, babban sakataren kwamitin zartaswa na hukumar 'yancin kai ta kasar Falesdinu Saeb Erekat ya ce, ana fatan shugaba Trump zai iya aiwatar da "shirin kasashen biyu" yadda ya kamata, ya kuma jaddada cewa, ya kamata gwamnatin kasar Amurka ta gane muhimmancin warware matsalar Falesdinu, inda yake sa kaimi ga sabuwar gwamnatin kasar Amurka da ta matsa lamba ga Isra'ila, domin ta tsayar da gina matsugunin Yahudawa. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China