Za a yi taron shugabanni game da yarjejeniyar yin rigakafin kwararowar hamada karo na 13 a Mongolia ta gida
Mataimakin shugaban hukumar kula da kare dazuka na kasar Sin Zhang Yongli, ya bayyana a yau Lahadi cewa, za a kira taron masu kulla yarjejeniyar kan rigakafin kwararowar hamada ta MDD karo na 13 a watan Satumbar wannan shekara a yanki mai cin gashin kansa na Mongolia ta gida na kasar Sin, inda bangarori 195 masu kulla yarjejeniyar za su tura wakilai kimanin 1400 zuwa taron, domin tattaunawa kan yadda za a yi rigakafi kwararowar hamada a duniya baki daya. (Maryam)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku