in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bukaci kasashen dake kudu da hamadar Sahara da su karfafa dabaransu na kulawa da filaye
2016-11-23 10:18:34 cri

Kwararru masu ilmin muhalli sun yi kira ga gwamnatocin kasashen dake kudu da hamadar Sahara da su karfafa dabarunsu na kulawa da filaye domin kiyaye muhallin halittu da kuma karfafa ci gaban tattalin arziki da na jama'a.

Masanan sun yi wannan kira ne a ranar Talata a yayin rufe taron ministocin albarkatun muhalli na kasashen gabashi da kudancin Afrika, a birnin Kigali.

Rwanda ta karbi bakuncin wannan dandali daga ranar 21 zuwa 22 ga watan Nuwamba da ya shafi bullo da hanyoyin amfani da kimiyya da fasaha wajen kulawa da filaye, ta yadda za a fifita tattalin arziki, kare muhalli da ba da kulawa yadda ya kamata ga filaye a cikin shiyyar.

Da yake magana a yayin wannan taro, Hussein Farah, tsohon darekta janar na cibiyar shiyya-shiyya kan taswirar albarkatu domin ci gaba (RCMRD), ya bayyana cewa, cimma da karfafa dabarun dake fifita kulawa da albarkatu cikin karko na filaye a kasashen Afrika dake kudu da hamadar Sahara zai taka muhimmiyar rawa domin kiyaye muhallin halittu da karfafa ci gaban tattalin arziki.

Dabarun kulawa da filaye da suka dace za su kasance masu muhimmanci domin aiwatar da muradun bunkasuwa cikin karko da kuma yarjejeniyoyin da aka cimma kan sauyin yanayi, in ji jami'in.

Mista Farah ya jaddada cewa, wani taimako mai karfi na albarkatun filaye, har ma da samunsu, rarraba su, sake tsugunnar da al'ummomi da bunkasa ababen more rayuwa, suna da muhimmanci domin gaggauta ci gaban al'umma da tattalin arzikin yankunan kasashen dake kudu da hamadar Sahara mafi fama da talauci. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China