Dokar harajin dai ta kiyaye muhalli, ta tanaji ka'idoji masu nagarta, kan yadda za a rika biya harajin kiyaye muhalli, wadanda suka shafi kamfanonin dake fitar da kayayyaki masu gurbata muhalli, da kuma wadanda ba sa ajiye sharar masana'antu mai illa yadda ya kamata a nan kasar Sin, ko kuma yankin dake karkashin ikon kasa ta Sin.
Haka kuma, an kafa ka'idoji kan yadda za a rika karbar haraji kan gurbataccen ruwa, da abubuwan shara da masana'antar tace gurbataccen ruwa, da masana'antar daidaita abubuwan shara suka fidda fiye da kima.
Za a fara aiwatar da wannan doka ta harajin kare muhalli ne tun daga ranar 1 ga watan Janairun shekarar 2018. (Maryam)