Mahukuntan kasar Sin sun tuhumi jami'ai da yawan su ya kai a kalla 687, bisa laifuka masu alaka da sakaci ko karya dokokin kare muhalli a sassan kasar daban daban.
Wata sanarwa da ma'aikatar kare muhalli ta kasa ta fitar a jiya Talata ta nuna cewa, a karshen watan Nuwambar da ya gabata, gwamnati ta tura rukunin masu bincike 7 zuwa larduna da biranen kasar 7 da suka hada da birnin Beijing, da Shanghai da kuma lardin Guangdong, a wani mataki na bincikar zarge zarge masu nasaba da karya dokokin kare muhalli.
Sakamakon hakan, an kai ga yanke hukuncin tara ta kimanin dalar Amurka miliyan 9 da dubu dari 6, kan laifuka da yawan su ya kai 1,479 cikin zarge zarge 1,893 da aka bincika.
Kaza lika sanarwar ta bayyana cewa, a zagaye na farko na binciken da aka gudanar, an samu jami'an wasu larduna 8 su 3,287 da laifuka iri daban daban, ciki hadda ba da izinin yin gine gine a wuraren da ba su dace ba, da wadanda ke iya gurbata muhalli, matakin da ya sanya wasu daga jami'an rasa mukaman su.
Matakin gwamnatin Sin na kare muhalli dai na kunshe cikin shirin shekaru biyar biyar karo na 13, wanda ya fayyace matakan shawo kan gurbatar iska, da ruwa, da kuma kasa a dukkanin fadin kasar baki daya.(Saminu)