Kome ya kammala domin baiwa Najeriya damar kafa tashoshin gwajin hayaki domin gudanar da gwajin a kai a kai na hayakin da motoci suke fitarwa a kan hanyoyin motocin kasar, in ji ministar muhallin Najeriya, Amina Mohammed a jiya Litinin.
Idan an kafa wadannan tashoshin, kuma an fara aiki da su, wannan zai taimaka wajen rage hayakin da motoci suke fitarwa da kashi 90 cikin 100, in ji ministar a yayin wani dandalin da cibiyar sanya ido kan aikin aiwatar da ka'idoji da dokoki ta kasa (NESREA) ta shirya a birnin Abuja.
Ministar ta bayyana cewa, shirin kasa na sanya ido kan hayakin da motoci suke fitarwa (NVECP), wani shiri ne da aka tsara domin sanya ido kan hayakin motoci.
Haka kuma, an tsara wani shiri ne domin daukar nauyin hayakin da wasu cibiyoyin injuna suke fitarwa, in ji ministar, tare da jaddada cewa, gwamnatin Najeriya za ta kafa wani kwamitin da zai aiki cikin hadin gwiwa tare da hukumomi domin jagorantar wannan shiri.
Madam Amina Mohammed ta yi kira ga dukkan bangarori masu ruwa da tsaki da su hada karfinsu tare da hukumomin gwamnati domin rage barazanar gurbacewar iska. (Maman Ada)