in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na shirin raba gwamnati da hukumomin tantance muhalli
2016-12-15 10:50:34 cri

Mahukuntan kasar Sin sun sha alwashin raba sassan gwamnati da hukumomin dake lura da ayyukan tantance yanayin muhalli, nan da karshen wannan shekara da muke ciki.

Hakan dai, a cewar ma'aikatar muhallin kasar, na da nasaba ne da burin da ake da shi na tabbatar da gudanar ayyukan wadannan hukumomi bisa adalci, ba kuma tare da tsoma hannu daga gwamnati ba.

A cewar mataimakin shugaban hukumar kare muhallin kasar ta Sin Huang Runqiu, tuni irin wadannan hukumomi guda 337, wadanda a baya ke da alaka da kananan hukumomi suka samu cin gashin kan su, aka kuma soke lasisin wasu, yayin da wasu 13 za su daina aiki nan da karshen wannan wata na Disamba.

Tun farkon shekarar 2015 ne dai aka umarci irin wadannan hukumomi na lura da yanayin muhalli, da su katse duk wata alaka da sassan gwamnati kafin kashen wannan shekara ta 2016, a wani mataki na kaucewa aikata almundahana, ko cusa son zuciya cikin ayyukan su. Tun kuma cikin shekarar ta 2015, 8 daga wadannan hukumomi suka aiwatar da hakan.

Kasar Sin dai na da irin wadannan hukumomi 984, da injiniyoyi dake aiki a fannin har 19,700, adadin da ya karu da kaso 90 bisa dari, idan aka kwatanta da na shekarar 2010.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China