in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kenya ta samu tallafin AfDB don samar da ruwa da tsabtar muhalli
2016-11-10 10:02:30 cri

Bankin raya ci gaban kasashen Afrika AfDB, ya amince zai baiwa kasar Kenya kudi kimanin dala miliyan 391 domin tallafawa shirin samar da ruwan sha, da kuma tsabtar muhalli na kasar Kenyan.

Shirin samar da ruwa da tsabtar muhalli a garuruwan kasar Kenya, an shirya shi ne da nufin samar da tsabtaccen ruwan sha ga manyan garuruwa 19, da kuma tsabtar muhalli a garuruwan kasar 17.

A wata sanarwa da bankin AfDB ya fitar a Nairobi, ya ce, shirin dai ya yi daidai da shirin kasar Kenya na raya ci gaban kasar nan da shekarar 2030, kuma kashi na biyu ne na shirin raya kasar na shekaru biyar biyar wato MTP-II, wanda manufarsa ita ce, samar da ingantaccen ruwan sha da kuma tsabtar muhalli.

Sanarwar ta kara da cewa, manufar shirin ita ce, domin ya habaka ci gaban tattalin arziki, da inganta rayuwar jama'a, da kuma tallafawa shirin tinkarar sauyin yanayi.

Ana sa ran shirin zai samarwa mutane sama da miliyan 2 da dubu 100 tsabtataccen ruwan sha, sannan ya samarwa mutane sama da miliyan 1 da dubu 300 kariya daga cututtukan da ake dauka ta hanyar ruwa, kuma zai samar da sabbin guraben ayyukan yi sama da dubu 15 ga al'ummar kasar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China