in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rahoton zargin da Amurka ta yiwa Rasha na sa hannu cikin babban zabenta ya bata ran kasar Rasha
2017-01-10 10:28:23 cri
Sakataren kula da harkokin labarai na shugaban kasar Rasha Dmitri Peskov ya bayyana a jiya cewa, rahoton da hukumar leken asiri ta kasar Amurka ta bayar, inda take zargin kasar Rasha da tsoma baki cikin babban zaben shugaban kasar Amurka ta intanet ya bata ran kasar Rasha kwarai da gaske, sa'an nan, ya ce, rahoton babu gaskiya cikinsa, jami'ai da hukomomin kasar Rasha ba su taba kai hari ga kasar Amurka ta intanet ba.

A ranar 6 ga wata ne, hukumar leken asiri ta kasar Amurka ta fidda wani rahoto, inda ta bayyana cewa, kasar Rasha ta sa hannu cikin babban zaben shugaban kasar ta hanyar kai yin kutse ta intanet, domin rage amincewar al'ummomin kasar kan tsarin dimokuradiyyar kasa, da kuma kawo wa yar takarar jam'iyyar dimokuradiyya Hillary Clinton matsala.

Amma, a wannan rana, Donald Trump ya sanar da cewa, ba a sami matsala kan sakamakon babban zaben shugaban kasar ba. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China