in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Trump ya bukaci Obama ya yi watsi da batun sauyawa fursunoni daga gidan kurkuku na Guantanamo
2017-01-04 11:01:32 cri

Sabon zababben shugaban Amurka Donald Trump, ya bukaci gwamnatin Obama da ta yi watsi da shirinta na sauyawa fursunoni wajen zama daga gidan kurkuku na Guantanamo na sojoji dake kasar Cuba, inda ya bayyana wadanda ake tsare da su din a matsayin mutane dake da mummunan hadari.

Trumph, ya ce abu ne da ba zai taba yiwuwa ba a saki fursunonin daga Gitmo. Inda ya bayyana cewa babu dalilin da zai sa a baiwa fursunonin masu matukar hadari damar sake komawa bakin daga, kamar yadda ya sanar a shafinsa na Twitter.

Shi dai shugaban na Amurka mai barin gado Barack Obama, ya sha nanata aniyar sauyawa fursunonin yakin wadanda ake tsare da su, kana ya lashi takobin aiwatar da hakan zuwa karshe wa'adin mulkinsa a ranar 20 ga wannan wata.

Tun a lokacin yakin neman zabensa a shekarar da ta gabata, mista Trump, ya sha kalubalantar manufofin gwamnatin Obama game da rufe gidan yarin na Guantanamo.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China