Wadannan nasarori a cewar Obama sun hada da farfado da tattalin arzikin kasar bayan da ya fuskanci matsala a lokacin da ya hau mulki, bude sabon babi da kasar Cuba, cimma yarjejeniya game da shirin nukiliyar kasar Iran. Sauran sun hada da kisan Osama Bin Laden,halasta auren jinsi da kuma kara samar da shirin Inshoran kiwon lafiya ga 'yan kasar.
Bugu da kari, shugaba Obama ya tabo batun rashin daidaito a fannin biyan albashi, bambancin launin fata da na siyasa a matsayin manyan abubuwa guda uku da ke yiwa demokiradiyar Amurka barazana. A saboda haka, ya bukaci Amurkawa da su sauke nauyin da ke kansu na 'yan kasa.
A ranar 20 ga watan Janairu ne Donald Trump zai karbi jagorancin kasar ta Amurka daga hannun Barack Obama. Ana kuma saran a wannan rana ce Trump zai yi ganawarsa ta farko da manema labarai a birnin New York.(Ibrahim)