Maria Zakharova, ta soki gwamnatin Amurka kan samar da makamai ga dakarun da ba sa ga-maciji da gwamnatin Siriya, inda ta ce, hakan ba shi da bambanci da danyen aiki da masu kisa suka yi, kuma yana kawo barazana ga tsaron sojojin Rasha da jami'an diplomasiyyar Rasha wadanda ke aiki a kasar ta Siriya.
Game da tsarin kakkabo makamai masu linzami da Amurka ta kafa, Maria Zakharova ta ce, Amurka ta kan bayyana cewa wai tana fuskantar barazanar makaman nukiliya daga kasashen Iran da Koriya ta Arewa, shi ya sa ta girke tsarin kakkabo makamai masu linzami. Amma gaskiyar labarin shi ne, gwamnatin Amurka a wani yunkurin take na samun fifiko kan kasar Rasha wajen nuna karfin nukiliya.
Bugu da kari kuma, Zakharova ta soki gwamnatin Amurka kan yunkurin yawaita nata salon demokuradiyya a fadin duniya, da matsawa gwamnatocin sauran kasashe lamba bisa hujjar kare hakkin bil'adama.(Murtala Zhang)