in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An zartas da sabon jerin sunayen mambobin majalisar ministoci a Cote d'Ivoire
2017-01-12 10:20:31 cri
Jiya Laraba 11 ga wata, shugaban kasar Cote d'Ivoire Alassane Ouattara ya sa hannu kan takardar umurnin shugaba, inda ya zartas da sabon jerin sunayen mambobin majalisar ministocin sa, wadda sabon firaministan kasar Amadou Gon Coulibaly ya tsara. Sa'an nan, an gabatar da jerin sunayen a yayin taron maneman labaran da aka yi a wanann rana.

Sabuwar majalissar ministocin ta kunshi mambobi guda 29, ciki har da sabon sakatare mai kula da harkokin ba da horaswa kan ayyuka, da samar da ilimin fasahohi. Haka zalika, an ce gaba daya akwai mata 5 cikin sabuwar majalissar, sa'an nan, akwai sabbin 'yan majalissar 8 da suka shiga majalisar a karon farko. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China