in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Cote d'Ivoire tana son yin koyi da tsarin kasar Sin domin cigabanta
2016-10-03 13:17:08 cri
Kasar Cote d'ivoire dake fatan bunkasa tattalin arzikinta zuwa shekarar 2020 na da niyyar koyi da tsarin kasar Sin wadda cigaban tattalinta cikin sauri ya kasance daya daga cikin abubuwa mafi janyo hankali a cikin wadannan shekaru talatin na baya bayan nan, in ji ministan man fetur da makamashi na kasar Cote d'Ivoire, Adama Toungara.

Cote d'Ivoire na sa ido da sanya hankali sosai kan cigaban kasar Sin daga dukkan fannoni, kuma tana da niyyar koyi da tsarin Sin, in ji mista Adama Toungara a albarkacin bikin cikon shekaru 67 da kafa jamhuriyyar jama'ar kasar Sin da aka shirya a ranar Asabar a birnin Abidjan.

A cewar mista Toungara, kasar Sin tana burgewa bisa ga al'amarinta na samun cigaban tattalin arziki cikin sauri, haka kuma ministan ya bayyana kyaukyawar huldar dangantaka da abokantaka dake tsakanin Sin da Cote d'Ivoire, wadda take kasancewa wani babban alheri ga Cote d'Ivoire bisa hanyarta ta neman cigaba.

Cote d'Ivoire na fatan yin amfani da damammakin da Sin take dasu domin bunkasa tattalin arzikinta, in ji mista Toungara.

Haka kuma jami'in ya nuna yabo kan kokarin da Sin ta yi a fannoni daban daban domin cigaban tattalin arziki da na al'ummar Cote d'Ivoire, ta hanyar musammun ma gina filin wasannin motsa jiki na Olympic a birnin Abidjan, zamanintar da tashar ruwan Abidjan, shirin fadada da sake gina layin wutar lantarki, gyara wani sabon yankin tattalin arziki a Abidjan, tare da ayyukan gyaran hanyoyi. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China