in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kura ta lafa a kasar Cote d'Ivoire
2017-01-09 10:34:32 cri
Bisa labarin da kafofin watsa labaru na kasar Cote d'Ivoire suka bayar a jiya Lahadi, an ce, ministan kula da harkokin tsaron na fadar shugaban kasar Alain Richard Donwahi, ya kammala shawarwari tsakaninsa da wakilan sojojin masu bore na Bouake dake tsakiyar kasar a daren ranar 7 ga wata, da kuma koma birnin Abidjan. A halin yanzu, kura ta lafa kuma an samu kwanciyar hankali a Abidjan da Bouake da sauran wuraren da rikice-rikice suka faru.

Kakakin sojojin da suka tada boren, ya yi alkawari bayan shawarwarin cewa, za a tabbatar da bin doka da oda a kasar a dukkan fannoni tun daga ranar 8 ga wannan wata. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China