in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Guillaume Soro ya sake lashe zaben shugaban majalisar dokokin Cote d'Ivoire
2017-01-10 11:09:04 cri
Jiya Litinin 9 ga wata, Guillaume Soro ya sake lashe zaben shugaban majalisar dokokin kasar Cote d'Ivoire wanda aka yi a watan Disambar shekarar 2016.

Guillaume Soro daya ne daga cikin 'yan takara guda biyu, wadanda suka tsaya takarar zaben shugaban majalisar dokokin kasar na wannan karo.

Yayin zaman majalisar dokokin kasar da aka yi a birnin Abidjan, mambobin ta 230 daga jimillar 252 ne suka nuna goyon bayan su ga Guillaume Soro, lamarin da ya ba shi damar lashe zaben shugaban majalisar dokokin kasar. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China