in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Cote d'Ivoire ta kaddamar da wani gagarumin aikin soja domin kawar da matsalar kungiyoyi masu fashi da makamai
2016-09-12 11:11:26 cri

Hukumomin tsaron Cote d'Ivoire sun sanar a ranar Asabar da fara wani gagarumin aikin soja da ya shafi magance matsalar kungiyoyi masu dauke da makamai dake cin karensu ba babbaka a kan hanyoyin kasar.

A cewar Youssouf Kouyate, mataimakin darekta janar na 'yan sandan kasar, an baiwa jami'an tsaro umurnin da su tabbatar da tsaron hanyoyin mota daga kungiyoyi masu dauke da makamai da ake kira "masu tare hanya", na dakile su har inda suka boye.

Mutane dubu uku da suka hada da 'yan sanda, jardarma, sojoji, tare da motoci da kayayyakin sadarwa masu dama, aka yi amfani da su, in ji kwamishina Kouyate.

Haka kuma, aikin na da manufar yaki da tashe-tashen hankali a cikin birane ta hanyar ba da kariya a muhimman wuware kamar makarantu, bankuna da wuraren kasuwanci, in ji wannan ofisa.

Hare hare kan jami'an tsaro da fararen hula na cigaba da karuwa a cikin kasar. Domin yaki da wannan annoba, shugaban kasar Cote d'Ivoire Alassane Ouattara ya sanar da daukar nagartattun matakai, tare da jaddada cewa jami'an tsaro ba za su nuna tausayi ba ga kungiyoyi masu dauke da mamakai dake tare jama'a a kan hanyoyin kasar. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China