in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An tayar da bore a wani sansanin soja na Cote d'Ivoire
2017-01-08 13:53:29 cri
Jiya ranar Asabar, sojoji a wani sansanin dake gabashin Abidjan, cibiyar tattalin arzikin kasar Cote d'Ivoire suka yi bore, ya zuwa yanzu babu labarin mutuwar mutane ko jikkatarsu a sakamakon wannan rikicin.

A daren ranar Asabar din, shugaban kasar Alassane Ouattara ya yi kira ga dukkan sojojin da suka tayar da boren, da su koma sansaninsu, kana ya amince da yin la'akari da bukatunsu game da kudin rangwame da kyautatta halin zaman rayuwa da dai sauransu.

Ouattara ya bayyana haka ne a yayin da yake jawabi a wajen taron musamman na mistoci da aka yi a wannan rana.

Ma'aikatar tsaron kasar Cote d'Ivore ta bayar da labari cewa, a safiyar ranar 6 ga wannan watan, wasu sojojin gwamnati dake birnin Bouake dake tsakiyar kasar suka mamaye hukumar birnin da ofisoshin 'yan sanda guda biyu, tare kuma da datse muhimman hanyoyin shiga da fita daga birnin.

A wani labari na daban da kafofin watsa labarun kasar suka bayar, an ce ya zuwa yammacin ranar 7 ga wata, an samu irin boren da sojoji suka tayar a sauran wasu yankunan kasar, ciki har da Daloaa dake yammaci da tsakiyar kasar, Korhogo da Odienné dake arewacin kasar, Daoukro dake gabashin kasar, Duekoue da Toulepleu dake yammacin kasar da dai sauransu.

A ranar 6 ga wata, minista dake kula da harkokin tsaron kasa na fadar shugaban kasar Alain Richard Donwahi ya bayyana cewa, gwamnatin kasar ta yi kira ga dukkan sojojin da su kai zuciya nesa, su kuma sake komawa sansaninsu, domin warware matsalolin da abin ya shafa a cikin rundunar soja. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China